Rukuni na 17 na tawagar likitocin kasar Sin da ke Botswana, ya gudanar da ayyukan kiwon lafiya kyauta tare da ba da gudummawa ga kungiyar ceton yara, watau SOS Children’s Village a kauyen Tlokweng da ke wajen Gaborone, babban birnin kasar wacce take kudancin Afirka.
A jawabin da ya gabatar a wajen taron, darektan kungiyar ta SOS Children’s Village ta Botswana, Motshwari Kitso, ya nuna matukar jin dadinsa kan tallafin da kungiyarsu ta samu daga ofishin jakadancin kasar Sin da ke Botswana da kuma al’ummar Sinawa mazauna kasar a tsawon shekaru.
- Yakin Iran Da Isra’ila Ya Haifar Da Tashin Farashin Litar Man Fetur A Nijeriya
- Sin Na Fatan Kwamitin Sulhun MDD Zai Goyi Bayan Kuduri Game Da Halin Da Iran Ke Ciki
Ita dai SOS Children’s Villages Botswana, kungiya ce mai zaman kanta da ke tallafa wa yara da matasa wadanda suka rasa samun kulawar iyaye ko kuma wadanda ke fuskantar matsalar hakan, inda take gudanar da cibiyoyi uku a kauyen Tlokweng na gundumar Kudu maso Gabas, da birnin Francistown na Gundumar Arewa maso Gabas, da kuma garin Serowe na Gundumar Tsakiya.
A yanzu haka, kungiyar tana kula da kimanin yara 320 a cibiyoyinta guda uku kuma tana tallafa wa karin yara 1,500 da ke cikin al’ummomi, kamar yadda Kitso ya bayyana. Kana ta ce, tana sa ran samun karin ayyukan jin kai a nan gaba a sauran cibiyoyinsu biyu da kuma cikin al’ummomin da ke kewaye.
Shugaban al’ummar yankin, Lazarus Ikalafeng, ya yi maraba da zuwan tawagar likitocin kasar Sin da ayyukansu na kiwon lafiya da wayar da kai, wadanda ke karfafa gwiwar jama’a da su ba da fifiko ga kula da lafiyarsu ta hanyar zuwa ganin likita. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp