Kasafin kudi na birnin tarayya Abuja (FCT) na shekarar 2025, kimanin naira tiriliyan 1.78 da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya aike wa Majalisa, ya tsallake karatu na biyu.
Shugaba Tinubu ya gabatar da kudirin kasafin FCT na 2025 ta wata wasika da ya aike zuwa ga shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, inda ya bukaci ‘yan majalisar su gaggauta amincewa da kudirin domin saukaka aiwatar da muhimman ayyukan raya kasa a babban birnin kasar.
- Yadda Aka Gina Ofishin ‘Yansanda Na Zamani A Abuja
- Sojoji 20 Sun Ɓace Bayan Harin Da ISWAP Suka Kai Marte
Da yake karanta wasikar a zauren majalisar a ranar Laraba a Abuja, Akpabio ya bayyana cewa, gabatar da takardar ya yi daidai da sashe na 299 na kundin tsarin mulkin kasar, wanda ya bai wa shugaban kasa ikon mika kudirin kasafin kudin FCT ga majalisar dokokin kasar domin tantancewa da kuma amincewa.
Tinubu ya bayyana cewa, an tsara kasafin ne domin bunkasa muhimman sassa da suka hada da kiwon lafiya, jin dadin al’umma, noma, da kuma samar da ayyukan yi.
Shugaban ya bayyana cewa, kashi 85 cikin 100 na kasafin za a kashe su ne wajen kammala ayyukan more rayuwa da ayyukan raya kasa, inda aka ware kashi 15 cikin 100 domin aiwatar da sabbin tsare-tsare.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp